(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya bayyana cewa za’a gudanar da sallar Idi a cikin wuraren addini na unguwanni a kasar Iran, amma ba a masallatan idi kamar yadda aka saba ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Asabar a lokacinda yake jawabi a gaban kwamitin yaki da cutar Corona a kasar a nan birnin Tehran.
Shugaban ya kara da cewa za’a gudanar da sallar idin ne tare da kiyaye matakan kiwon lafiya wadanda kwamitin yaki da cutar Corona ya bayyana. Sannan za’a gudanar da sallar ce a wuraren da babu hatsarin yaduwar cutar Corona a kasar.
Har’ila yau shugaban ya ce a nan Tehran za’a gudanar da jerin gwanon ranar Qudus kamar yadda aka saba, amma a wannan karon rundunonin dakarun kare juyin juya halin musulunci ne za su shirya jerin gwanon motoci don raya wannan rana mai muhimmanci.
/129
17 Mayu 2020 - 08:00
Lambar labari: 1037606
Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya bayyana cewa za’a gudanar da sallar Idi a cikin wuraren addini na unguwanni a kasar Iran, amma ba a masallatan idi kamar yadda aka saba ba.